Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya ruwaito cewa: Wannan mutum, mai suna Kourosh Kiwani, IRGC ta kama shi a Savojbolagh a ranar 16 ga watan Yunin shekara 2025.
Kamar yadda aka fada, Kiwani ya tuntubi wani jami'in Mossadi mai suna "Ben" wanda ya ke jin yaren Farisanci a 1402 ta hanyar yanar gizo. Jami'in Mossad ya gayyaci Kiwani don ganawa a Berlin, yana samun bayanai game da halinsa na sirri da na kudi.
A wannan taron, baya ga kudaden tafiye-tafiye, an biya wa Kiwani kudi kuma a tsawon lokacin aikinsu tare, an biya masa kudade daban-daban. A lokacin da aka kama shi, an kama wasu tsabar kudi, motoci, babura da kayan leken asiri a hannun sa.
Ra'ayinka